Jami’ar Bayero ta ɗaga likkafar ma’aikatanta 772

Jami'ar, Bayero
BUK Senate 1

Kwamitin gudanarwar Jami’ar Bayero ta Kano, ya amince da ɗaga likkafar ma’aikatanta ta 772 da suka ƙunshi na sashen koyarwa da na gudanarwa.

Hakan na ƙunshe ne cikin wata sanarwa mai ɗauke da sa hannun babban sakataren yada labaran jamiar Lamara Garba wadda aka rabawa manema labarai a Kano.

Jaridar Solacebase ta rawaito cewa jami’in yaɗa labaran jami’ar Lamara Garba na cewa “Bisa miƙo daftarin karin girma na 2021 da shugaban Jami’ar Bayero Farfesa Sagir Adamu Abbas ya yi, kwamitin gudanarwar jami’ar ya amince da daga likafar malaman”

Lamara Garba ya ƙara da cewa an ɗaga likkafar malamai 8 zuwa muƙamin farfesa, sai 18 zuwa matakin Associate Professor, sai kuma ma’aikata 747 waɗanda ba malamai ba da aka yi musu ƙarin girma zuwa manyan mukamai.

Sanarwar ta ce, ƙarin girman da aka yiwa malamai da ma’aikatan, zai fara aiki ne nan take.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here