NDA ta kaddamar da kananan sojoji 453

BBF6DA1E 8135 4DC7 9C87 389CD2B35D25
BBF6DA1E 8135 4DC7 9C87 389CD2B35D25

A yau Alhamis ne makarantar horas da sojoji ta Najeriya NDA ta kaddamar dalibai 453 wanda zasu yu kwas na 75.

A yayin taron wanda an rantsar da daliban wanda hakan ya tabbatar da su a matsayin cikakkun daliban makarantar.

Da yake jawabi a wajen taron tsohon shugaban makarantar Farfesa Shehu Abdullahi wanda shi ne babban bako na musamman  ya bukaci daliban da su dauki karatunsu da horon aikin soja da muhimmanci domin kuwa suna suna tafiya ne kafada-kafada.

Ya ce yawancin daliban makarantar wanda suke da hazaoa suna samun nasara a bangaren horon soja, don haka akwai bukatar rungumar layin horon guda biyu da muhimmanci.

Abdullahi ya ce fanni yaki da ayyukan sojoji a karni na 21 yana bukatar sabbin tunani da kirkire-kirkire da aka kafa bisa basira da fasaha.

Da yake jawabi Shugaban makarantar ta NDA Manjo Janar Ibrahim Yusuf, ya ce tuni suka fara horas da daliban  aikin soji bisa tsarin karatun da aka yi wa kwaskwarima da aka tsara domin ba su ilimi da kwarewa don tunkarar barazanar da ke addabar kasar.

A cikin makonni takwas da suka gabata, daliban sun samu horon soji mai tsauri da aka tsara don sanya su zama lafiyayyan hankali da kuma lafiyar jiki don shiga cikin tsauraran tsarin horar da sojoji da ilimin ilimi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here