Gwamnatin Tarayya ta yi barazana da takunkumi kan ma’aikatan Gwamnati

Folasade Yemi Esan, gwamnati, tarayya, takunkumi, barazana, ma'aikata
Gwamnatin tarayya ta ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ta fara wani yunkuri na ganin cewa ba'a fallasa wasu takardu na gwamnati da aka kebe a...

Gwamnatin tarayya ta ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya ta fara wani yunkuri na ganin cewa ba’a fallasa wasu takardu na gwamnati da aka kebe a matsayin masu muhimmanci ga jama’a ba.

Wannan yana kunshe ne a cikin wata sanarwa da aka ɗora a yanar gizon ofishin shugaban ma’aikatan gwamnatin tarayya wanda aka rubuta a ranar 19 ga watan Fabrairun 2024.

A cewar sanarwar, shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya Dakta Folashade Yemi-Esan ta ce fallasa irin wadannan takardu ya zama abin kunya ga gwamnati don haka ya zama abin da ba za’a amince da shi ba.

Karanta wannan: Mayaƙan Fano sun ƙwace wani babban gari a Habasha

Sanarwar ta cigaba da cewa, “Wannan abin kunya ne ga gwamnati don haka ba za’a amince da shi ba, a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin hana wannan ci gaban da ba’a so, duk sakatarorin dindindin za su hanzarta tafiyar da ƙaura zuwa tsarin aiki na dijital da kuma tabbatar da tura ingantaccen maganin gudanar da abubuwan kasuwanci.

“Bugu da ƙari, an shawarci sakatarorin dindindin da su gargaɗi dukkan ma’aikata game da zazzagewa da rarraba bayanan hukuma da takardu, duk wani jami’in da aka kama yana aikata irin wannan rashin adalci, za’a yi masa hukunci mai tsanani daidai da tanadin da ya dace na dokokin ma’aikatan gwamnati da sauran da’irori.”

Karanta wannan: Kotu ta bada umarnin yiwa Murja gwajin kwakwalwa

An samu karuwar kwararar wasu muhimman takardu na gwamnati a ‘yan kwanakin nan, a kwanakin baya ne wata sanarwa daga ofishin sakataren gwamnatin tarayya George Akume, ta bayyana shirin ware kudi Naira 500 a matsayin alawus-alawus ga mambobin kwamitin uku na mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta kafa.

Haka kuma an ga wata takarda ta makudan kudade da za’a ware a matsayin tallafin aikin Hajji wanda aka ce ya fito ne daga ofishin ministan kudi Wale Edun.

Takardun bayanan biyu sun haifar da bacin rai a tsakanin kungiyoyin farar hula da kungiyoyin kwadago da ke neman a binciki irin wannan rabon.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here