Hukumar yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa NDLEA, ta kama wani matashi Muhammad Muhammed dan shekara 22 da yake kai wa ‘yan fashin daji miyagun kwayoyi a Kano.
Jami’an NDLEA sun kama wanda ake zargin yana sintiri a kan hanyar Bichi zuwa Kano yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa Katsina dauke da ampoules 277 na allurar pentazocine daure a cinyarsa da kuma sashin jikin sa da Salatif.
Karin karatu: Buba Marwa ya kaddamar da barikin NDLEA da cibiyar gyaran hali
Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan yada Labarai na Hukumar NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar a Abuja ranar Lahadi.
“An kama shi ne a ranar Lahadi, 13 ga Afrilu, yayin da aka kama Mohammed Abdulrahman da Abdulaziz, mai shekaru 43, a rana guda a yankin Research da ke Rimin Kebe a karamar hukumar Nasarawa, tare da skunk 68, nau’in tabar wiwi mai nauyin 30kg,” in ji sanarwar.













































