Shugaban hukumar korafe-korafe da yaki da cin hanci da rashawa ta jihar Kano, Muhuyi Rimin-Gado a ranar Laraba ya kalubalanci dakatarwar da aka yi masa a gaban kotun masana’antu ta kasa.
Rimin-Gado ya shigar da karar ne yana kalubalantar dakatarwar da gwamnatin jihar Kano da wasu mutane biyar suka yi masa.
Wadanda aka shigar karar sun hada da Babban Lauyan gwamnatin Kano, Majalisar Dokokin Jihar Kano, Akanta Janar Kano.
Sauran sune mukaddashin shugaban hukumar Mahmud Balarabe da kwamishinan ‘yan sandan Kano a matsayin wadanda ake tuhuma na daya da na biyu da na uku da na hudu da na biyar da na shida.
Lauyan da ya shigar da kara, Muhammad Tola, ya shaida wa kotun cewa an sanar da dukkan bangarorin, amma har yanzu ba sun ki bayyana domin yin sharia’ar.
Ya kuma shaida wa kotun cewa yana da wasu bayanai guda biyu da ya ke son janyewa.
A martaninsa, Abdulsalam Saleh, lauyan wadanda ake tuhuma na daya da na biyu da na hudu ya ce sun shigar da takardar shaidar gabatar da shari’a.
Bugu da kari Saleh ya bayyana cewa suna shirin shigar da karar zuwa sashin kotun na Kano.
A karshe Alkalin ya bayar da umarnin a gabatar da sanarwar sauraren karar ga wanda ake kara na shida, kwamishinan ‘yan sandan Kano, wanda bai halarci kotun ba.
A gaskiya ma, Majalisar Dokokin Jihar Kano ta dakatar da wanda ke da’awar a matsayin shugaban hukumar a ranar 5 ga Yuli, 2021.













































