A ranar Lahadi ne shugaban kasa Muhammadu Buhari zai bar Abuja zuwa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 77 (UNGA77).
Cikin wata sanarwa da mai bawa Shugaban Kasar shawara na musamman kan harkokin yada labarai, Femi Adesina ya fitar, ta ce Buhari zai kuma gabatar da makala ga majalisar a ranar Laraba, 21 ga watan Satumba.
“Shugaban zai kuma gudanar da wasu ayyuka guda biyu kafin ya dawo kasar nan a ranar Litinin 26 ga watan Satumba 2022,” in ji sanarwar.
“Shugaba Muhammadu Buhari zai bar Abuja, Lahadi, 18 ga watan Satumba, zuwa birnin New York na kasar Amurka domin halartar taron shekara-shekara na shugabannin duniya a Majalisar Dinkin Duniya (UNGA77).
Taken taro a bana Wanda shi ne karo na 77 da aka bude tun a ranar Talata, 13 ga watan Satumba shi ne: “Lokaci mai cike da rudani: Hanyoyin kawo Canji ga Kalubalen da ke tsakanin juna.”
“Muhimman batutuwan da aka tattauna a taron na Majalisar Dinkin Duniya (UNGA) na bana sun hada da; yakin Ukraine da rikicin makamashi da batun sauyin yanayi sai batun kan yadda za a kawo karshen cutar COVID-19, da kuma babban taron koli kan yadda za a kawo sauye-sauye a fannin Ilimi.
“Shugaba Buhari zai gabatar da nasa jawabin a rana ta biyu da fara gudanar da muhawara.
“Bayan bayanin nasa, shugaban kasar zai kuma halarci wasu manyan tarurrukan da suka hada da na kungiyar hadin gwiwar tattalin arzikin kasa da kasa ta Najeriya (NIEPF), wadda Najeriya ta kira tare da hadin gwiwar kungiyar ‘yan kasuwa (BCIU).
“A cikin tawagar shugaban kasa akwai uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari da wasu gwamnoni da ministoci da manyan jami’an gwamnati.
Sanarwar ta ce “Ana sa ran shugaban zai dawo kasar a ranar Litinin, 26 ga Satumba.”













































