“Buhari ya kasance mai tawadi’u kuma adalin shugaba” – Garba Shehu

WhatsApp Image 2025 07 15 at 09.48.45 723x430

Yayin da ake shirin jana’izar tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari a Daura, tsohon mai taimaka masa, Garba Shehu, ya bayyana shi a matsayin shugaba mai koyi da gaskiya, rikon amana da adalci.

Ya bayyana hakanne a yayin hirarsa da wakilin SolaceBase a Daura a yau Talata, yana mai cewa babbar rayuwa ba ta damu mirgayi Buhari ba duk da kasancewarsa tsohon shugaban kasa.

Shehu ya ce Buhari yayi rayuwa mai sauƙi ba tare da sha’awar dukiya ba, kuma bai taɓa karɓar ko bayar da cin hanci ba.

Ya ƙara da cewa Buhari bai taɓa sauya maslahar ƙasa da son zuciya ba.

Shehu ya buƙaci shugabanni su koyi darasi daga rayuwarsa, yana mai cewa ya rayu da tunanin komawa ga Allah.

Ya roƙi Allah ya gafarta masa, ya kuma jaddada cewa babu abin da ya fi adalci ga shugabanci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here