Ko a gaban Allah zan bada shaidar Buhari mutumin kirki ne – Pantami

WhatsApp Image 2025 07 15 at 12.53.15 750x430

 

Tsohon Ministan Harkokin Sadarwa, Farfesa Isa Ali Ibrahim Pantami, ya bayyana cewa ya shafe sama da shekaru 24 yana tare da tsohon Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, kuma bai taɓa shakkar akan ɗabi’unsa kyawawa ba.

Pantami ya tabbatar da cewa yana da tabbaci kuma zai iya ba da shaidar halayen Buhari har a gaban Allah.

Wakilin SolaceBase ya rawaito cewa Pantami ya bayyana hakan ne a ranar Talata a gidan Buhari da ke Daura, yayin da ake shirin karɓar gawar tsohon shugaban ƙasar.

Ya ce, “Ina da kusanci da shi tun kafin rasuwarsa. Ko a lokacin da yake shugabanci, na kan ziyarce shi a gidansa har cikin ɗakin zama. Wannan ya nuna yadda muke da kusanci sosai.”

Ya ƙara da cewa, “’Ya’yansa suna girmama mu kuma suna mu’amala da mu tamkar ‘yan uwansu. Suna da tarbiyya matuƙa, yanzu nauyi ne a kanmu mu ci gaba da kula da su.”

Pantami ya ci gaba da cewa, “A tsawon shekaru na koyi darussa masu yawa daga gare shi—tarbiyya, gaskiya, da rikon amana.

“Ya kasance ɗan ƙasa mai matuƙar kishin ƙasa. Ina iya ba da shaida a gaban Allah cewa mutum ne na amana.”

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here