Gwamnatin tarayya za ta binciki harin jirgin sama da ya kashe mutum 10 a Sokoto – Ministan Tsaro

Matawalle, Eid-El-Fitr, addu'a, tsaro, minista, karami, zaman lafiya
Karamin Ministan Tsaro, Dakta Bello Matawalle, ya bukaci al’ummar Musulmi da su ci gaba da yiwa Najeriya Addu'o'in samun zaman lafiya da tabbatar da tsaro...

 

Gwamnatin Tarayya ta sha alwashin gudanar da cikakken bincike kan harin bam da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 10 a kauyukan Gidan Bisa da Runtuwa na karamar hukumar Silame a jihar Sokoto.

Wannan tabbaci ya fito ne a ranar Juma’a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Gwamnan Jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya fitar.

A cewar sanarwar, Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya bayyana hakan yayin wata ziyarar ta’aziyya da ya kai wa Gwamna Ahmed Aliyu a Sokoto.

Matawalle ya bayyana lamarin a matsayin abin takaici matuka, yana mai tabbatar da cewa za a gudanar da bincike mai zurfi domin gano musabbabin lamarin da tabbatar da adalci.

“Shugaban kasa yana cikin damuwa kan abin da ya faru, kuma ya umarce ni in kawo ta’aziyyarsa tare da tabbacin gudanar da bincike na tsanaki,” in ji shi.

A nasa jawabin, Gwamna Ahmed Aliyu ya bukaci sojoji da su kara inganta hanyoyin tattara bayanan sirri da kuma amfani da kayan leken asiri don kauce wa irin wannan matsala.

Ya kuma yaba wa hukumomin tsaro bisa kokarinsu na kare lafiya da dukiyoyin al’umma, tare da nuna godiya ga Shugaban Kasa Bola Tinubu kan nuna damuwarsa game da lamarin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here