Mutum 3 sun mutu sakamakon ambaliyar ruwa a Nairobi

Nairobi, mutum, mutu, ambaliyar, ruwa
Ana fargabar cewa akalla mutum uku sun rasa ransu a wata ambaliyar ruwa da ta afku a Nairobi, babban birnin Kenya. Daga cikin waɗanda suka rasu har da wani...

Ana fargabar cewa akalla mutum uku sun rasa ransu a wata ambaliyar ruwa da ta afku a Nairobi, babban birnin Kenya.

Daga cikin waɗanda suka rasu har da wani jami’in ɗan sanda da yake ƙoƙarin ceton wasu iyalai da suka maƙale a yankin Kamakunji.

Wasu hotuna da bidiyo da aka sanya a kafafen sada zumunta sun nuna yadda mutane a cikin ababen hawa ke tsaye cirko-cirko saboda motocinsu sun maƙale sakamakon ruwan da ya mamaye tituna a birnin.

Karin labari: An gurfanar da mutane 4 kan zargin garkuwa da malaman Jami’a da Yara a Abuja

Rahotanni sun ce wani ɓangare na babbar hanyar Nairobin ma ta shafe da ruwa.

Masu hasashen yanayi dai sun ce za’a ci gaba da samun mamakon ruwan sama nan da wasu kwanaki masu zuwa a birnin na Nairobi.

Tuni dai mahukunta suka shawarci mazauna wuraren da ke da haɗarin fuskantar ambaliyar ruwan da su bar wajen.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here