Ku Dai Na Amfani Da Sunana Kuna Cutar ‘Yan Najeriya – Sufeto Janar Na ‘Yan Sandan Ya Gargadi Jami’ai

IGP kayode egbetokun 1

Sufeto Janar na ‘yan sandan kasa (IGP) Kayode Egbetokun ya ce jami’an ‘yan sandan da aka samu da laifin amfani da sunansa wajen cutar ‘yan Najeriya za su fuskanci hukunci mai tsanani.

Jami’in hulda da jama’a na rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi, ne ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar da ta gabata, yayin da ya koka kan yadda wasu jami’an ‘yan sanda ke ci gaba da nuna rashin da’a, wanda a cewarsa, ke zubar da mutunci da martabar rundunar.

“Duk da gargadin da ake yi da kuma daukar matakan ladabtarwa a kan wadanda aka fallasa, har yanzu wasu jami’an na ci gaba da aikata wannan abin kunya da ke zubar da mutuncin jama’a.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here