Shugaban ma’aikata na gwamnan jihar Kwara, Prince Abdul Kadir Mahe, ya rasu.
Mahe, Basaraken Masarautar Ilorin kuma sakataren dindindin mai ritaya, ya rasu a safiyar ranar Asabar.
An tabbatar da labarin rasuwar Mahe a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun babban sakataren yada labaran gwamnan, Rafiu Ajakaye.