Kwamitin Naɗi da Ƙarin Matsayi, na Jami’ar Bayero ta Kano (BUK) ya amince da ɗaga likkafar Injiniya Dakta Umma Abdullahi zuwa matsayin Farfesa a fannin Injiniyancin gine-gine wato ‘Mechanical Engineering’.
Amincewar, wadda aka yi a jiya Juma’a, ta fara aiki ne tun daga ranar 1 ga watan Oktoba, 2023.
A halin yanzu dai Farfesa Umma ta zama Farfesa mace ta farko a fannin Injiniya daga Arewacin Najeriya, kuma Farfesa mace ta uku a fannin a Najeriya.