Jakadan kasar Sin a Najeriya Mista Cui Jianchun ya ce, kasarsu na shirin jagorantar samar da alluran rigakafin cutar COVID-19 a Najeriya
A wani taron tattaunawa da jakadan a fadar mulkin Najeriya ta Villa wanda cibiyar nazari da bincike ta kasar Sin ta shirya mai taken ‘Gina kyakkyawar alaka tsakanin Sin da Najeriya la’akari da irin gudunmawar da Najeriyar ke bayarwa.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya ya rawaito cewa, taron tattaunawar na zuwa ne la’akari da irin cigaban da aka samu a taron zubeban kwarya da aka gudanar tsakanin kasar Sin da kasashen Afrika a birnin Dakar, na ƙasar Senegal.
Mista Cui ya kuma ce, ƙaddamar da cibiyoyin samar da rigakafin cutar na da alaka da irin kokarin da Najeriya da wasu ƙasashen Afirka ke yi na yaƙi da cutar, hakan ta sanya Shugaban ƙasar Xi Jinping amincewa kasashen su cike giɓin ƙarancin rikagafin da ake samu don su ma su dogara da kansu
Jakadan ya ce, Shugaba Xi Jinping a taron Majalisar ministoci karo na 8, ya ce, gwamntin Sin za ta yi aiki da kamfanonin kasar tareda takwarorinsu na Afirka don Samar da rigakafi milyan 400 a Najeriya
“Ina fatan a samarda rigakafi Kimanin Milyan 1000 Wanda cikin wannan adadi, Sin Zata bada gudunmawar rigakafi kimanin Milyan 600, yayin da sauran Milyan 400 za a samar da su ta hanyar hadin gwiwa tsakanin gwamntin Sin da Nahiyar Afrika” inji Xi Jinping
Sanarwar ta rawaito Jakadan Sin a Najeriya nacewa lokaci yayi da kasashen biyu zasuyi amfani da damar dan amfanar juna ta fannin kasuwanci ba wai samarda rigakafi kadai ba.
“Kunga Muna gabatar da tsare tsare domin sake nazari yadda za a murkushe barazanar wannan cuta Kuma wajibi ne a tabbatar da tsare gaskiya dan samun hadin kan kasashen biyu” inji jakadan
A tsokacin da ya gabatar babban daraktan cibiyar nazarin binciken tsakanin kasashen Mista Charles Onunaiju, ya yaba wa gwamntin Sin bisa irin gudun mawar da take bai wa Najeriya da Nahiyar Afrika baki ɗaya.













































