Shugaban kasa Muhammadu Buhari a daren ranar Talata ya karbi bakuncin tsohon ministan tsaro, Theophilus Yakubu Danjuma a fadar shugaban kasa ta Villa.

Ba a bayyana dalilin ziyarar ta Danjuma ba, a cikin hotunan da fadar Shugaban kasa ta fitar.
Ko da yake mai daukar hoton shugaban kasar Sunday Aghaeze a ranar Laraba ya ce ganawar ce ta sirri.
Danjuma ya kasance ministan tsaro a zamanin gwamnatin tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo.
Ya zama daya daga cikin masu sukar gwamnatin shugaba Buhari kan halin da al’umma ke ciki, musamman kan rashin tsaro.
Tsohon ministan tsaron ya zargi gwamnatin Najeriya da sojojin kasar da hannu a rikicin Fulani makiyaya a fadin kasar.












































