Wata ƙungiya mai zaman kanta mai suna Khalifa Dankade wadda aka fi sani da KDC Foundation, ta ce, ta kammala shirye-shiryen horas da Almajirai kusan 6,000 sana’o’i a faɗin jihohin Arewa 6 domin dogaro da kai da ilimi mai inganci.
Wanda ya kafa ƙungiyar Khalifa Usman Dankade ne ya bayyana hakan a Talata makon nan yayin wata ziyara da ya kai ofishin jaridar Solacebase da ke Kano.
Dankade ya ce gidauniyar KDC wadda aka kafa a shekarar 2014, tana hada kai da gwamnatoci a dukkan matakai wajen ganin an gyara tsarin Almajirci.
Ya ce ƙungiyar wajen cimma wannan buri tana jan hankalin masu ruwa da tsaki musamman kafafen yaɗa labarai domin wayar da kan jama’a tare da wayar da kan al’umma da gyara tsarin na Almajiranci.
Dankade ya yaba da rawar da Solacebase ke takawa wajen inganta ayyukan jinƙai da tallafa wa ayyukan al’umma.

”Kafar yaɗa labaran ku ta zama dandali mai matukar alfanu da kuma karɓuwa da ke yaɗa sahihai kuma labarai na gaskiya,” in ji Khalifa Dankade.
”Saboda haka muna neman haɗin gwiwar ku don aiwatar da wannan sabon aikin
namu mai taken ɗakin karatu na Al’umma kashi na 3 wanda aka fara a watan Satumba”.
“Tsarin aiki ne da ofishin jakadancin Amurka da ke Abuja ke tallafawa yana gudana ne a jihohi 6 da suka haɗa da Kano da Jigawa da Katsina da Sokoto da jihar Neja da kuma Zamfara”.
A cewarsa, za a zabo Almajiri 100 daga makarantu goma a jihohin da aka zaɓa domin gudanar da shirin.
Ya bayyana cewa aikin zai duba tare da tabbatar da tsarin karatun makarantun Tsangaya don daidaitawa tare da hada muhimman abubuwan da za su tabbatar da Almajiri ya dogara da kansa bayan kammala karatunsa.
A nasa ɓangaren, mamallakin kamfanin jaridar Solacebase kuma babban jami’in gudanarwa na kamfanin Fridabs Solacebase Communication Ltd, Abdullateef Abubakar Jos, ya yaba da wannan shiri na gidauniyar wanda ba ƙaramin abu ba ne da zai magance ƙalubalen da ake fuskanta a tsarin Almajirci.

Haka kuma, Ya bayyana shirin jaridar ta Internet na yin aiki da gidauniyar domin cimma manufofin da aka sanya a gaba.













































