Mataimakin Shugaban Ƙasa, Kashim Shettima, ya yabawa Jami’ar Bayero, Kano (BUK), bisa jajircewarta wajen ba da ingantaccen ilimi da aiwatar da tsarin karɓar ɗalibai na adalci ga kowa ba tare da bambancin addini ko kabila ba.
Shettima, wanda Dr. Nurudeen Zauro ya wakilta, ya yi wannan jawabi yayin ƙaddamar da Taron Tunawa da Kammalawa na Ƙungiyar Ɗaliban BUK ta 2004 a jami’ar.
Ya jaddada muhimmancin haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu zaman kansu don samar da ci gaba mai ɗorewa.
Haka zalika, ya bukaci mahalarta taron su yi amfani da basirarsu don kawo sauye-sauye masu amfani a cikin al’umma.