Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu ta fara daukar sabbin dalibai na shekarar 2024/2025

KHAIRUN Kano 750x430

Yanzu haka an bude tashar shigar da dalibai na shekarar 2024/2025 a Jami’ar Khalifa Isyaku Rabiu (KHAIRUN), Kano.

A wata sanarwa da jami’ar ta fitar ta hannun Bilal Dahiru Tijjani a ranar Laraba, ya ce daliban da suka zabi jami’ar a matsayin zabinsu na farko kuma suka samu maki 140 ko sama da haka a jarabawar JAMB na shekarar 2024 za su iya ziyartar shafin makarantar domin cike kwasakwasan digiri na farko.

Sanarwar ta kuma bukaci daliban da tun farko ba su zabi KHAIRUN a matsayin zabinsu na farko ba da su ziyarci ofishin JAMB tare da karbar katin gyara domin sabunta zabin su ga KHAIRUN.

Yadda ake Aikatawa:

1. Ziyarci tashar shiga: [https://admission.khairun.edu.ng/#/apply](https://admission.khairun.edu.ng/#/apply)

2. Ƙirƙiri asusu ta amfani da ingantaccen adireshin imel.

3. Cika fam ɗin aikace-aikacen kan layi.

4. Loda takaddun da ake buƙata.

5. Biyan kuɗin aikace-aikacen.

6. Gabatar da aikace-aikacen ku. Don ƙarin bayani, ‘yan takara za su iya tuntuɓar ofishin shiga a 07063759985 ko 08119159989, ko ziyarci gidan yanar gizon jami’a a [www.Khairun.edu.ng](https://www.khairun.edu.ng).

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here