Kano: An samu hatsaniya tsakanin ‘yan Hisbah da wasu matasa a unguwar Sabon Gari

DF7098F3 DEF3 4C87 B07E 0DA319DDAEC6
DF7098F3 DEF3 4C87 B07E 0DA319DDAEC6

A daren jiya Talata ne aka samu hatsaniya tsakanin jami’an hukumar Hisbah ta Kano da wasu matasa a wata mashaya dake unguwar Sabon Gari a cikin garin Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa jami’an hukumar Hisbah sun dira a wani wajen shaye-shaye mai suna Ballat Hughes dake Court road a cikin unguwar Sabon Gari domin kwace giya da sauran kayan shaye-shaye.

Lamarin da ya fusata matasan da suke wajen har ta kai ga sun fara jifan ‘yan Hisbah tare da fasa kwalaben giya, wanda ya kai ga samun hatsaniya a wajen.

Shaidun gani da ido sun tabbatar da cewa bayan faruwar lamarin, ‘yan daba da wasu bata gari sun yi amfani da wannan damar inda suka sace wasu muhimman kayayyaki a wajen.

Jaridar Solacebase ta ruwaito cewa jihar Kano ta hana sha da siyar da giya a ciki da wajen jihar, kasancewar Kano tana amfani da shari’ar musulunci.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here