Sarkin Daura mai shekaru 90 ya auri matashiya ƴar shekaru 20

Emir of Daura Faruk Umar Faruk with the new bride Aisha Iro Maikano
Emir of Daura Faruk Umar Faruk with the new bride Aisha Iro Maikano

Sarkin Daura Alhaji Faruk Umar Faruk, ya auri amaryar sa  ƴar shekara 20 mai suna Aisha Iro Maikano a ranar Asabar ɗin da ta gabata.

An dai haifi angon sarkin ne a shekarar 1931, wanda kuma aka ɗaura masa sabon auren a garin Katsina bayan da suka samu fahimtar juna ta ƴan kwanaki tsakaninsa da amaryar tasa

Rahotanni sun bayyana cewa, sarkin ya biya kudin sadakin auren har naira miliyan ɗaya ga amaryar wadda ƴa ce ga Fagacin Katsina Alhaji Iro Maikano.

Haka kuma rahotonni sun ce, sarkin ya auri matasan mata ƙasa da 4 a cikin shekaru 6 da suka gabata.

Wani matsakaicin  faifan bidiyo ya nuna yadda Magajin Garin Daura Alhaji Musa Umar, ya wakilci sarkin a wajen ɗaurin auren.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here