Wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne sun kashe dalibai biyu a jihar Kwara

Offa Poly
Offa Poly

Wasu da ake zargin ’yan kungiyar asiri ne a Federal Polytechnic, Offa a jihar Kwara a ranar Alhamis sun kashe dalibai biyu na Higher National Diploma (HND) 1

Yayin da har yanzu ba a tantance daya dalibi namiji ba, sai dayan da abin ya shafa ita ce Miss Toyin Bamidele ta tsangayar kimiyya da fasaha.

An tattaro cewa dalibin da aka kashe shi ne shugaban kungiyar asiri na makarantar, an kashe shi a harabar makarantar ta su.

Rundunar ‘yan sandan jihar Kwara ta baza jami’anta a cikin garin domin kamo wadanda suka aikata wannan aika aika tare da gurfanar da su gaban kotu, hukumar gudanarwar ta makarantar ta jajantawa iyalan Miss Toyin Bamidele a wata sanarwa da mukaddashin jami’in hulda da jama’a na kwalejin ya fitar. , Mrs Folake Akinloye.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here