Wasu da ake zargin mayakan Boko Haram ne sun kai hari kan ayarin motocin gwamnan jihar Yobe, Mai Mala Buni a kan hanyar Maiduguri zuwa Dramaturg, inda suka kashe ‘yan sanda biyu tare da raunata wasu biyu.
An kai harin ne a ranar Asabar bayan da gwamnan ya halarci taro karo na 24 na jami’ar Maiduguri da ke jihar Borno.
A cewar wani ganau da ke cikin tawagar amma ya nemi a sakaya sunansa, maharan sun bude wuta kan ayarin motocin daga bangarorin biyu na babbar hanyar.












































