Kungiyar lauyoyi ta kasa ta yi Allah wadai da tube babban Jojin Jihar Osun Justice Adepele Ojo, da gwamnan Jihar Ademola Adeleke, ya yi.
A wata sanarwa da sakataren yada labaran kungiyar ta NBA na kasa, Mista Akorede Lawal, ya fitar a ranar Asabar, kungiyar ta ce ba za ta amince da mai shari’a Olayinka Afolabi ba, a matsayin mukaddashin babban Jojin da gwamnan ya nada.
Sanarwar ta ce NBA ta dogara ne da kundin tsarin mulkin kasa wanda ya bawa bangaren shari’a yancin cin gashin kai.
Sakataren yada labaran kungiyar na kasa ya ce matakin da gwamnan ya dauka ba wai kawai ya yi fatali da yancin cin gashin kai na bangaren shari’a bane, har ma da yin watsi da umarnin kotu.
Lawal ya ce kungiyar ta yi Allah wadai da matakin da ya saba wa doka, inda ya kara da cewa tsige wani Babban Jojin Jihar daga mukaminsa, karan tsaye ne ga tanade-tanaden kundin tsarin mulkin kasa da aka yiwa kwaskwarima a 1999.
A cewarsa, kungiyar NBA ta damu matuka ganin yadda gwamnatin Osun ta zabi yin watsi da doka da kuma kin bin umarnin da kotun masana’antu ta kasa da ke Ibadan, babban birnin jihar Oyo ta bayar.
Lawal, ya kuma ce kungiyar NBA ba za ta amince da Mai Shari’a Afolabi a matsayin babban jojin jihar Osun ba.
Gwamna Adeleke ya tsige babban jojin ne bisa zargin rashin da’a da cin zarafi sai zargin cin hanci da rashawa da kuma rashin bin doka da oda.