Matatar man fetur na Dangote ta sanar da sake rage farashin tsohon man fetur da take da shi
Yanzu dai an kayyade sabon farashin kan kowacce lita a kan Naira 835, wanda a baya ake sayarwa a Naira 865, wanda ya fara aiki kwanaki shida da suka gabata, hakan ya nuna an samu raguwar kashi 3.5 cikin 100.
Kamfanin ya sanar da daidaita farashin ga abokan cinikinsa ta hanyar sanarwar hukuma ranar Laraba.
Labari mai alaka: Matatar Dangote ta rage farashin man fetur
Wannan rage farashin na baya-bayan nan ya nuna rangwame karo na uku da matatar Dangote ta yi a kasa da makonni shida.
Tun da farko dai matatar man ta rage farashin daga naira 880 zuwa naira 865 a kowace lita, duk da cewa fa’idar faduwar farashin bai bayyana a fanfunan man ba, domin ‘yan kasuwar sun gaza rangwantawa mabukata ragin kudaden.