Fursunoni 62 sun kammala karatun boko zaman su na gidan yari a Kano

IMG 20250417 WA0016 750x430

Hukumar da ke kula da gidajen ajiya da gyaran hali ta kasa NCoS ta ce ta yaye fursunoni 62 a karkashin shirinta na ci gaba da ba da ilimi a jihar Kano.

Daliban da aka yaye sun rubuta jarrabawar (NECO) da (NBAIS).

Kwanturolan hukumar na jihar Kano Ado Inuwa ne ya bayyana haka a wajen bikin yaye dalibai da aka yi ranar Alhamis a Kano.

Ya ce shirin ya yi daidai da dokar NCoS ta 2019 da tsarin gyaran zamani, wanda ya baiwa fursunonin damar ci gaba da karatunsu da koyon sana’o’in hannu a lokacin da suke tsare.

Inuwa ya ce an shirya shirin ne domin gyara fursunonin don zama ’yan kasa nagari bayan an sake su daga tsare.

Karin karatu: KNUPDA ta rushe shagon yar Tiktok Rahama Sa’idu kan yin gini ba bisa ka’ida ba

Ya yaba wa Babban Kwanturola na hukumar (CGC), Sylvester Ndidi Nwakuche, bisa goyon bayan da yake bayarwa wajen kyautata jin dadin fursunonin tare da sanya su cikin shirye-shiryen ilimi da na sana’a.

Ta kuma yaba wa Gwamna Abba Kabir-Yusuf bisa goyon bayan da yake baiwa fursunonin da ke samun damar ci gaba da karatunsu tare da inganta aikin kiwon lafiya a wuraren da ake tsare da su a jihar.

Har ila yau, Kabir-Yusuf ya jaddada kudirin tallafa wa Hukumar don bunkasa ilimin tsare-tsare domin amfanin ’yan gidan yari.

Sakataren gwamnatin jihar Umar Ibrahim-Faruk ya wakilci gwamnan, inda ya bayyana farin cikinsa kan yadda aka samu nasarar gyara fursunonin ta hanyar ba su karatun boko. (NAN)

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here