Wata gobara ta tashi a shagon yar TikTok din nan Rahama Saidu, dake kan titin UDB a karamar hukumar Tarauni a jihar Kano.
SolaceBase ta ruwaito cewa lamarin ya faru ne sa’o’i kadan bayan da Hukumar (KNUPDA) ta gudanar da wani aikin rusau a wani bangare na shagon, bisa dalilin tsawaita gine-ginen ba bisa ka’ida ba.
Ko da yake har yanzu ba a san musabbabin tashin gobarar ba, sai dai wani ganau da ya yi magana da manema labarai a wurin a daren ranar Alhamis, ya ce gobarar ta tashi ne sakamakon wata tartsatsin wutar lantarki da ta taso.
Shaidan gani da ido ya bayyana cewa wani mai shagon da ke makwabtaka da shi ya dauki injiniyoyin walda don gudanar da gyare-gyare a shagonsa, wanda shi ma rusau din KNUPDA ta shafaa.
Labari mai alaƙa: KNUPDA ta rushe shagon yar Tiktok Rahama Sa’idu kan yin gini ba bisa ka’ida ba
“Bayan rushewar, Rahama ta zo ta kwashe dukkan kayanta daga shagon, abin takaici, gobarar ta tashi ba da dadewa ba.”
An gano cewa, baya ga shagon Rahama, shagon mai daukar hoto ma ya tashi da gobarar.
Sai dai an ga ‘yan sanda sun mamaye wurin domin hana wawure dukiyar jama’a.