Da Dumi-Dumi: Gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin jirgin saman Najeriya na wani lokaci

Nigeria Air, Gwamnatin, tarayya, dakatar, aikin, jirgin saman, Najeriya, lokaci, tinubu, hadi, sirika, Festus, Keyamo
Gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin jirgin saman Air Najeriya har zuwa wani lokaci. Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a...

Daga: Sunusi A. Dantalata Fagge

Gwamnatin tarayya ta dakatar da aikin jirgin saman Air Najeriya har zuwa wani lokaci.

Ministan Sufurin Jiragen Sama Festus Keyamo ne ya sanar da hakan a wajen taron Ministoci na cika shekarar gwamnatin Tinubu daya kan mulki.

Ya ce, kamfanin jirgin bai taba zama na Najeriya ba, sai dai yunkurin yin amfani da wani jirgin sama na kasar waje domin ya nuna a matsayin jirgin saman Najeriya.

Karin labari: Kotun daukaka kara ta tabbatar da nasarar Diri a matsayin Gwamnan Bayelsa

Idan dai za a iya tunawa, a shekarar 2023, ma’aikatar sufurin jiragen sama, karkashin Hadi Sirika, tsohon minista, ta kaddamar da jirgin Najeriya Air kwanaki uku kafin karshen gwamnatin tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

Ci gaban ya haifar da damuwa a tsakanin masu ruwa da tsaki a duk fadin kasar game da tsarin mallakar wanda ya baiwa kamfanin jiragen saman Habasha kashi 49 cikin dari.

Gwamnatin tarayya ta samu kashi 5 cikin 100 na hannun jari, yayin da kungiyar masu zuba jari ta Najeriya uku ke da kashi 46.

Karin labari: Gwamnan Kano Yusuf Ya Ba Da Umarnin Chafke Tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero

Da ta ke mayar da martani kan yarjejeniyar a watan Yunin 2023, Majalisar Wakilai ta bukaci gwamnatin tarayya da ta dakatar da ayyukan kamfanin na Najeriya Air, inda ta bayyana shi a matsayin ‘damfara’.

A watan Agusta 2023, Keyamo ya ba da sanarwar cewa an dakatar da aikin jigilar kayayyaki na kasa har sai an sanar da shi.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here