Kungiyar Cinema Exhibitors Association of Nigeria ta ce ta samar da kudin shiga da ya kai Naira miliyan 482 daga gidajen kallo na cinema dake Najeriya.
Shugaban kungiyar, Mista Opeyemi Ajayi ne ya bayyana hakan ya yin hirar sa da kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a jihar lagos.
Ya kara da cewa gidajan kallo Najeriya sun sami karin masu shiga sosai a watan Yuli ne sakamakon hutu da yawa da aka samu a watan.
Ya kuma yi kira ga yan Najeriya da su cigaba da shiga gidajan kallo domin samun nishadi.