Gwamnatin jihar Bauchi ta kore wani babban sakataren ma’aikatar fansho ta jihar, Ibrahim Garba, sakamakon kamashi da lefin cin kudin wani dan fansho daya mutu.
Sanar da korar tasa na kunshe cikin wata sanarawa da jami’in yada labarai na hukumar ta fansho a jihar, malam Saleh Umar ya fitar a Bauchi ranar Talata.
Hukumar ta zarge shi da karya dokar aiki mai lamaba ta (PSR) 0327(XI) wacce tai wukunci akan cin kudin gwamnati da almubarzaranci.
“Hukumar fansho ta amunci da korar Ibrahim Garba a zaman ta na goma 17 da tai ranar 1 ga watan Ogusata.”
“Kwamatin ladaftarwa na hukumar fansho ya kama Garba da lefin satar kudin gwamnati ta hanyar musanya lambar asusun ajiyar Audu Mohammed da nasa bayan ya sami labarin mutuwar sa.”
“Daga nan ya dinga karbar kudin duk wata na tsawan shekaru hudu da wata bakwai, wanda kudin da ya karba sun kai naira miliyan uku.”
Sanarwar ta kara da cewa za’a cire kudin da ya dinga karba daga cikin hakkunanshi da za’a bashi bayan korar tasa.













































