Matsalar tsaro: gwamnionin Arewa da Sarakunan gargajiya sun goyi bayan kafa rundunar ‘yan sandan jihohi, sun nemi a dakatar da hakar ma’adinai na wata shida

Northern governors (1)

Gwamnonin jihohi 19 na Arewa tare da shugabannin sarakunan gargajiya na yankin sun gudanar da taro a Kaduna, inda suka fitar da mahimman matakai domin magance ƙara ta’azzarar matsalolin tsaro da ke addabar yankin.

Taron, wanda aka yi a gidan Sir Kashim Ibrahim, ya haɗa majalisar gwamnonin artewa da kuma majalisar Sarakunan gargajiya ta Arewa domin tattauna manyan matsalolin da ke shafar yankin da ƙasar gaba ɗaya.

A cikin sanarwar bayan taron, shugaban majalisar gwamnonin Arewa gwamna Inuwa Yahaya ya bayyana cewa shugabannin sun ƙara jaddada muhimmancin haɗin kai da zaman lafiya a cikin yankin.

Karanta: Da ɗumi-ɗumi: Ministan tsaron Najeriya ya yi murabus daga muƙamin sa

Sanarwar ta kuma nuna cewa shugabannin sun goyi bayan samar da rundunar ’yan sanda ta jihohi a matsayin muhimmin mataki na ƙarfafa tsaro da rage yawaitar ayyukan ta’addanci da garkuwa da mutane.

Haka kuma shugabannin sun nemi a dakatar da aikin hakar ma’adinai na tsawon wata shida domin bada damar gudanar da bincike kan yadda ayyukan hakar ke taimakawa wajen ƙara tashin hankali a yankin.

Shugabannin sun jaddada cewa ana bukatar matakai na gaggawa da tsari mai dorewa domin sauya yanayin tsaro, tare da tabbatar da cewa dukkan hukumomi suna aiki tare don kare rayuka da dukiyoyin jama’a.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here