Tinubu na ci gaba da tafiyar da harkokin mulki daga kasashen waje, yanzu haka ya bar Paris zuwa London – Fadar shugaban kasa

Tinubu depart US 750x430

Fadar shugaban kasa ta ce shugaba Bola Tinubu na ci gaba da jagorantar al’amuran kasar nan daga Turai, duk da cewa ya shafe kusan makonni biyu a wajen kasar.

Shugaban zai dawo gida Najeriya bayan hutun Easter.

A cikin wata sanarwa da ya sanya wa hannu a ranar Alhamis, mai ba Tinubu shawara na musamman kan yada labarai da dabaru, Bayo Onanuga, ya bayyana cewa shugaban, wanda ya yi tattaki daga Paris zuwa Landan a karshen mako, “ya ci gaba da tsunduma cikin harkokin mulkin Najeriya” kuma yana tattaunawa tare da manyan jami’an gwamnati.

Karanta: Yanzu-yanzu: Gobara ta kone shagon yar TikTok Rahama Saidu a Kano

Onanuga ya kara da cewa shugaban kasar ya ba da umarni ga shugabannin tsaro don magance barazanar da ke kunno kai a wasu sassan kasar nan.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here