Tinubu ya umarci ma’aikatar shari’a da majalisar dokoki da su duba matsalolin kudirorin dokar haraji dan magance su

Bola Tinubu new new 750x430

 

Shugaban kasa Bola Tinubu ya umarci Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da Majalisar Dokoki ta Kasa su magance matsalolin da ke tattare da kudirorin sauyin haraji da aka gabatar.

Kudirorin, da aka mika wa Majalisar Dokoki ta Kasa kwanan nan, ya fuskanci suka daga jihohin arewa musamman gwamnoni, wadanda ke fargabar cewa sauyin zai iya cutar da yankinsu da kuma kara tabarbarewar tattalin arzikin Najeriya.

Tinubu ya bayar da umarni ga Ma’aikatar Shari’a da su hada kai da Majalisar Dokoki don warware batutuwan da ake takaddama kansu kafin kudirorin su zama doka.

Wannan umarni ya fito ne ta bakin Ministan Yada Labarai da Wayar da Kan Al’umma, Mohammed Idris, wanda ya bayyana cewa gwamnatin ta bude kofa don karbar ra’ayoyin da suka dace.

“Ya kamata a fahimci cewa babu wani abin da gwamnati ke boyewa da zai sa a ce ana gaggauta aiwatar da tsari ba tare da an tattauna ba,” in ji Idris.

“Gwamnatin Tarayya na maraba da shawarwari masu ma’ana don gyara duk wasu matsaloli a cikin kudirin.”

Ministan ya jaddada muhimmancin tattaunawa cikin lumana, inda ya bukaci ‘yan Najeriya su guji batutuwan kabilanci ko na bangaranci cikin wannan muhawara.

Ya karyata rade-radin cewa an yi kudirorin don kassara jihohin arewa, yana kira su da “labaran karya” da “bayani na kanzon kurege.”

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here