Tsohon shugaban ƙasar Kenya, Mwai Kibaki, ya rasu yana da shekaru 90 a duniya, kamar yadda shugaban ƙasar Uhuru Kenyatta ya bayyana.
Zaben da ya yi a shekara ta 2002 ya kawo ƙarshen mulkin jam’iyya daya da aka shafe shekaru 40 ana yi tun bayan samun ƴancin kai.
Sai dai kuma sake zabensa a shekara ta 2007 ya haifar da tashin hankali na tsawon watanni a faɗin ƙasar tare da haddasa mutuwar mutane aƙalla dubu ɗaya da ɗari biyu.
Shugaba Kenyatta ya jagoranci masu jimamin rasuwar tasa, yana mai cewa Mista Kibaki “ya ɗauki alhakin kare jam’iyya mai mulki” kuma ya samu “girmamawa da kauna” ga wannan al’ummar.
Shugaban ya ayyana zaman makoki har sai an binne Mista Kibaki, tare da bada umarnin yin ƙasa da tutoci i zuwa rabi daga yadda suke a baya.
Za a yi masa jana’iza tare da cikakken girmamawar soja, in ji shugaba Kenyatta.
Mista Kibaki ya yi fice ne a kan sauye-sauyensa bisa sassaucin ra’ayi, wanda ya farfado da tattalin arzikin ƙasar ta Kenya duk da haka an zarge shi da rashin yin abin da ya dace don magance cin hanci da rashawa.
Ya kuma gabatar da sabon kundin tsarin mulki a shekarar 2010 bayan da aka amince da shi da gagarumin rinjaye a zaɓen raba gardama na kasa, Wasu ne dai a wancan lokaci suka gabatar da shi a matsayin lamari mafi muhimmanci na siyasa a tarihin Kenya tun bayan da ta sami ƴancin kai daga Birtaniya a shekarar 1963.
Haka kuma marigayin shugaban a lokacin mulkinsa ya ɓullo da tsarin siyasa mai cike da ruɗani da iyakantaccen ikon shugaban ƙasa.
Sai dai al’ummar Kenya sun rabu gida biyu dangane da mulkinsa, inda wasu ke yabon Mista Kibaki da samar da hadin kan kasa, yayin da wasu ke mayar da hankali kan sake zabensa na 2007 da kuma tashin hankalin da ya biyo baya.
Marigayin dai, ya mutu ya bar ƴaƴa hudu.













































