Jami’an rundunar ’yan sanda a Jihar Katsina sun yi nasarar tare wata mota ƙirar Golf da ke ɗauke da tarin abubuwan fashewa masu matuƙar haɗari a wani shingen bincike da ke Koza a ƙaramar hukumar Daura.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar ’yan sandan jihar, DSP Abubakar Aliyu, ya fitar, inda ya bayyana cewa jami’an sun yi nasarar kama motar ne yayin wani aikin bincike bisa bayanan sirri.
Sanarwar ta nuna cewa jami’an sun kama motar ne a lokacin da wani mutum mai suna Jamilu Musa mai shekaru 40 ke tuƙata, inda binciken gaggawa ya kai ga gano guda 6,975 na na’urorin tayar da bam da aka ɓoye cikin dabara a cikin motar.
A cewar sanarwar, wanda ake zargin ya amsa cewa ya karɓi kayan ne daga wani mutum mai suna Najib, wanda ya tsere, a kan hanyarsa zuwa Kongolam a ƙaramar hukumar Mai’adua ta Jihar Katsina, daga Jihar Kano.
Binciken da aka ci gaba da yi ya kai ga kama wasu mutane biyu, Ibrahim Murtala da Sulaiman Muhammad, inda jami’an suka gano guda 7,500 na na’urorin tayar da bam na lantarki da buhuna 30 da rabi na sinadarin gelatine masu nauyin kilo 2,273.65 a hannunsu.
Sanarwar ta ƙara da cewa dukkan waɗanda ake zargin sun amsa laifin, kuma za a gurfanar da su gaban kotu da zarar an kammala bincike, yayin da rundunar ke ci gaba da ƙoƙarin cafke wanda ya tsere.
Rundunar ’yan sandan ta bayyana cewa wannan aiki ya yi daidai da umarnin Sufeton ’yan sandan ƙasa, Kayode Egbetokun, na ƙara sa ido da sintiri bisa bayanan sirri musamman a manyan hanyoyi.
Rundunar ’yan sandan Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin CP Bello Shehu ya ce, za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin al’ummar jihar.
NAN













































