Dan takarar gwamna na jam’iyyar APC a zaben Kano da aka gudanar a ranar Asabar, Nasiru Yusuf Gawuna, ya ce kamata ya yi hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba.
Gawuna ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai a ranar Talata, wanda aka gudanar a Kano.
Dan takarar gwamnan wanda ke tare da shugabannin jam’iyyar, ya bayyana mamakinsa kan yadda zaben ya gudana, a yanayi da matakai iri daya da na ‘yan majalisar dokoki guda 16 da aka gudanar a rana guda kuma hukumar zabe INEC ta bayyana cewa ba a kammala ba.
Jaemridar Solacebase ta rawaito cewa INEC da safiyar ranar Litinin ta bayyana Abba Kabiru Yusuf na jam’iyyar NNPP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan Kano da aka gudanar ranar Asabar.














































Toh shi gawuna ba yace zae dauki qaddara bane?sae yayi haquri ya dauki qaddarar in dae da gaske yake