‘Yan bindiga sun kara kai hari ofishin hukumar shirya zabe ta kasa INEC, dake kan titi Port Harcourt a cikin jihar Imo.
Jaridar solacebase a satin da ya gabata ta ruwaitu cewa an kaiwa ofishin INEC din dake karamar hukumar Orlu a jihar ta Imo hari.
An tattaro rahotanin cewa ‘yan bindigar wadan da suka kai kimanin mutu goma sun kai harin ranar Litinin da mislalin karfe uku na dare.
Mai magana da yawun hukumar yan sandan jihar, CSP Mike Abattam, ya tabbatar da faruwara lamarin, sai dai bai yi karin hasake akai ba.
Ya ce hukumar yan sandan jihar tana gudanar da binkice a halin yanzu, domin kamu wadan da suka tsere.
Yayin kai harin, yan bindigar sun latata abubuwa da dama a ofishin.













































