Cutar Lassa ta kashe ma’aikatan lafiya biyu, 15 sun kamu – NCDC

NCDC

Cibiyar Dakile Cututtuka Masu Yaɗuwa ta ƙasa (NCDC) a ranar Litinin ta nuna damuwa kan yaduwar cutar Lassa tsakanin ma’aikatan kula da lafiya.

Hukumar dakile cututtuka ta lura cewa zuwa yanzu, ma’aikatan lafiya biyu sun rasu, yayin da aka tabbatar da mutum 15 da suka kamu da cutar Lassa a tsakanin ma’aikatan kula da lafiya daidai lokacin da ake fargabar fuskantar wani sabon barkewar cutar da dabbobi ke yada wa.

A cikin wata sanarwa da aka fitar a ranar Litinin, NCDC ta nuna tausayinta ga ma’aikatan lafiya da abin ya shafa.

NSCDC ta kuma ce, an samu rahoton kamuwa da cutar tsakanin ma’aikatan lafiya a jihohi da dama, ciki har da wuraren da ake yawan samun cutar kamar Ondo, Edo, Bauchi, Taraba, Ebonyi, da Benue, inda aka gano wuraren da abin ya fi kamari har a matakin Karamar Hukuma.

A cewar hukumar NCDC na binciken musabbabin kamuwa da cutar tsakanin ma’aikatan lafiya don gano abin da ke haddasa yaduwar cutar da kuma hana samun karin masu kamuwa.

Sakamakon binciken baya-bayan nan ya nuna gibin hanyoyin kariya da hana yaduwar cutar, da kuma rashin lura da haɗarin kamuwa a wasu sassan.”

Waɗannan gibin sun haifar da dabarun hana yaduwar cutar da ba su dace da haɗarin kamuwa da cutar ba, wanda hakan ke haifar da mummunan sakamako.

Cutar Lassa, wacce dabbobi ke yada wa, cuta ce mai tsanani wacce ake yada ta ta hanyar bera da ake kira Mastomys.

Cutar tana yaduwa a Najeriya da wasu ƙasashen Yammacin Afirka.

Tun daga barkewar cutar ta ƙarshe a 2016, an samu ƙaruwarta a yawan lokutan barkewar cutar.

Mutane galibi suna kamuwa da cutar Lassa ta hanyar abinci ko kayan gida da suka lalace da fitsari ko najasa na bera, inda cutar take yaduwa a cikin jama’a a wasu sassan Yammacin Afirka.

Cutar Lassa tana yaduwa a Benin, Ghana, Guinea, Liberia, Mali, Sierra Leone, Togo, da Najeriya, amma watakila tana nan a wasu ƙasashen Yammacin Afirka ma.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here