Mazauna al’ummar Rorau da ke Karamar Hukumar Kazaure a Jihar Jigawa sun kaddamar da tsarin adana kudi na jama’a domin taimakawa gidaje wajen biyan kudin maganin gaggawa da kuma rage jinkirin neman magani.
Al’ummar garin suna bayar da gudummawar kudi kadan-kadan akai-akai cikin wannan asusun, inda ake samar da kudaden ga iyalai a lokutan gaggawa.
Wasu daga cikin mazauna yankin sun shaida wa kamfanin dillancin labarai na kasa (NAN) a ranar Talata a Kazaure cewa, shirin yana samar da wata hanyar tallafin kudi ga iyalai da ka iya fuskantar kalubalen tara kudin jiyya cikin kankanin lokaci.
Wata mazauniyar yankin, Malama Shamsiya Hadi, ta bayyana cewa wannan shiri ya taimaka wa al’umma garin wajen daukar mataki cikin gaggawa a lokacin rashin lafiya.
Ta kara da cewa mazauna garin suna ba da gudummawa gwargwadon ikonsu, inda ta kara da cewa ajiye kudin hadin gwiwar da ake adanawa yana saukaka wa al-umma samun kudi yayin larurar rashin lafiya ta gaggawa.
“Wani lokacin rashin lafiya na zuwa ne daidai lokacin da iyali ba su da kudi a hannu, amma da samun wannan shirin asusun tara kudi, mambobi za su iya samun taimako lokacin da bukatar kiwon lafiya ta gaggawa ta taso,” in ji ta.
Shi ma wani mazaunin garin, Balarabe Ibrahim, ya ce shirin ya karfafa hadin kai a tsakanin mazauna yankin, sannan ya taimaka wa iyalai wajen adana kudaden jiyyar da ba a yi tsammani ba.
Ya ce al-ummar garin sun fahimci cewa ko da kananan gudummawa na akai-akai za su iya yin amfani sosai lokacin gaggawa.
Ibrahim ya kara da cewa shirin ya kuma zaburar da mazauna yankin wajen daukar nauyin kula da rayuwar marasa karfi a cikin al’umma.
Haka kuma, Hinde Audu ta bayyana cewa shirin asusun ya rage wa iyalai matsin lambar ciyo bashi lokacin da suke bukatar kulawar lafiya ta gaggawa.
Ta ce wasu iyalai suna fuskantar wahalar tara kudi cikin sauri don kudin mota, kudin ganin likita, magunguna da sauran kudaden kiwon lafiya na gaggawa.
“Samun asusun ajiyar al’umma yana nufin cewa ba lallai ba ne mu jira sai wani ya sami kudi kafin mu nemi taimako. Tallafin zai iya zuwa ne a daidai lokacin da ake bukatarsa,” in ji Audu.
A nasa bangaren, Mamman Halliru ya ce shirin ya kara wayar da kai game da mahimmancin yin ajiya domin lokutan gaggawa.
Halliru ya ce al’ummar na fatan dorewar shirin tare da kara yawan masu shiga ciki domin karin mazauna yankin su amfana da shi.
Ya yi kira ga hukumomin gwamnati, kungiyoyi masu zaman kansu da sauran masu ruwa da tsaki da su karfafa shirye-shiryen da suka ginu a cikin al’umma domin taimaka wa iyalai marasa karfi wajen jure kudaden da suke kashewa daga aljihunsu lokacin gaggawa.
NAN ta rawaito cewa wannan shiri na asusun ajiyar al’umma yana nuna irin kokarin da mazauna karkara ke yi na samar da hanyoyin cikin gida don gudanar da matsalolin kudi na ba-zata, musamman wadanda suka shafi kiwon lafiya. (NAN)














































