Gwamnatin Jihar Kano ta yi watsi da rahotannin da ke cewa yara 50 sun mutu sakamakon bullar cutar sankarau (diphtheria) a Karamar Hukumar Rano ta jihar.
Rahoton, wanda aka danganta shi ga dan majalisa mai wakiltar Rano, Ibrahim Muhammad, inda ya yi ikirarin cewa cutar ta yi sanadiyyar mutuwar yara 50 a karamar hukumar.
Sai dai, Babban Daraktan Cibiyar Kula da Cututtuka ta Jihar Kano (KNCDC), Farfesa Muhammad Adamu Abbas, a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Jumma’a, ya bayyana wannan ikirari a matsayin mara tushe da zai rikita jama’a.
Farfesa Abbas ya amince cewa cutar ta bulla kuma ta lakume rayuka, sai dai ya ce adadin mamatan da ake yadawa ba shi da shaida a cikin bayanan sa ido na cibiyar.
Ya bayyana cewa bayanan da ake da su sun nuna cewa mutuwar mutane biyu kacal aka samu sanadiyyar cutar a Rano a shekarar 2026, yayin da aka sami jimillar mutuwar mutane 29 tsakanin watan Yulin 2023 zuwa Agustan 2026.
A cewarsa, cibiyar ta gano mutane 32 da suka kamu da cutar a Rano, inda aka kwantar da marasa lafiya 25 a Cibiyar Kula da Cutar Sankarau da ke Babban Asibitin Rano, yayin da aka kula da sauran guda bakwai a Asibitin Cututtuka Masu Yaduwa (IDH) da ke Kano.
Babban jami’in na KNCDC ya kara da cewa kashi 94 cikin dari na mutanen da cutar ta shafa ba su yi riga-kafi ba, sannan kashi 91 cikin dari sun makara kafin su tafi asibiti don neman magani.
Ya nuna damuwarsa kan jinkirin da ake samu wajen kai rahoton mutanen da ake zargin sun kamu da cutar zuwa cibiyoyin lafiya, inda ya jaddada cewa gano cutar da wuri da fara magani su ne mabudan dakile yaduwarta.
Farfesa Abbas ya kuma soki dan majalisar kan ikirari mara tushe ba tare da tuntubar mahukuntan da suka dace ba, ciki har da Ma’aikatar Lafiya ta Jihar Kano da kuma KNCDC.
Ya ce dan majalisar ya taba yin irin wannan ikirari mara tabbas a watan Oktoban 2025, inda ya kara da cewa irin wadannan kalamai na iya ruda jama’a tare da gurgunta kokarin da ake yi na sa ido da shawo kan cututtuka.
Babban Daraktan KNCDC ya ce cibiyar ta tura tawagar jami’ai zuwa yankunan da dan majalisar ya yi ikirarin cewa cutar ta shafa, sai dai har yanzu tawagar ta gaza tabbatar da mace-macen da aka ruwaito duk da tattaunawa da suka yi da mazauna yankunan.
Ya nuna shakuku kan yadda za a ce mutane 50 sun mutu ba tare da an kai rahoto ba ta hanyar tsarin sa ido kan cututtuka na cikin al’umma da ke akwai, wanda ya hada da sarakunan gargajiya, Jami’an Sa Ido da Bayar da Rahoton Cututtuka, Jagororin Mazabu, Masu Bayar da Rahoto na Cikin Gari, Masu Wayar da Kan Al’umma da Masu Sa Ido na Sa-kai.
A cewarsa, wadannan tsare-tsare suna kai rahotanni akai-akai ga KNCDC da sauran abokan hadin gwiwa na bangaren lafiya a matsayin wani bangare na tsarin sa ido kan cututtuka na jihar.
Farfesa Abbas ya ce KNCDC ta kuma yi kokarin ganawa da dan majalisar domin samun sahihan bayanai kan mace-macen da aka ruwaito, don gano ko an yaudare shi ne ko kuma zai iya ba da bayanan da za su jagoranci jami’an lafiya zuwa ga iyalai ko dangin wadanda ake zargin sun mutun.
Ya ce irin wadannan bayanai za su ba cibiyar damar gudanar da bincike na gaba, ciki har da binciken musabbabin mutuwa ta hanyar tambayoyi inda bukatar hakan ta taso, sai dai ya kara da cewa kokarin tuntubarsa har yanzu bai yi nasara ba.
Duk da haka, Babban Daraktan KNCDC ya jinjina wa Gwamnatin Jihar Kano da Gwamnatin Tarayya kan ci gaba da ba da tallafi wajen sa ido kan cututtuka da kuma daukar mataki cikin gaggawa lokacin da annoba ta bulla.
Ya jaddada kudurin cibiyar na karfafa sa ido, tabbatar da daukar mataki cikin sauri da kuma aiki da sauran masu ruwa da tsaki domin rigakafi da sarrafa bullar cututtuka a fadin jihar.















































