
Gwamnatin Najeriya ta ce kasar ta rasa likitoci sama da dubu 16 cikin shekaru biyar, saboda yadda likitocin ke guduwa don aiki a kasashen ketare.
Wannan na zuwa ne a dai-dai lokacin da ake samun karuwar likitocin da ke tsallake Najeriya zuwa ketare don aiki a can, bisa hujjar rashin kyawun yanayin aiki.
Da yake bayani a kafar talabijin ta Channels, ministan lafiya Farfesa Ali Pate ya ce likitoci dubu 55 ne kachal ke kulawa da marasa lafiyar da ke Najeriya mai yawan mutane sama da miliyan 200.
Karin labari: Ma’aikatan jami’o’i sun ƙuduri shiga yajin aiki a Najeriya
Farfesa Pate ya nuna takaicin sa kan yadda wannan matsala ke dulmiyar da Najeriya cikin karancin kwararrun likitoci da ke kulawa da cututtuka masu sarkakiya, sai dai ya jaddada cewa gwamnati na iya bakin kokarin ta wajen shawo kan wannan matsala.
Yawan jami’an lafiya a Najeriya da suka hadar da likitoci da ungozoma da kuma malaman jinya har ma da masu bada magunguna da jami’an gwaje-gwajen cututtuka da na samfurin jini bai zarta dubu 300 ba.











































