Ramadan: Sanata Barau ya yiwa Kasa addu’a tare da shirin tallafawa mabukata

Barau Jibrin, ramadan, sanata, kasa, najeriya, addu'a tallafawa, mabukata, shirin
Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi maraba da ganin ganin watan azumin Ramadan, biyo bayan ayyana ranar Litinin 11...

Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawan Najeriya, Sanata Barau I. Jibrin, ya yi maraba da ganin ganin watan azumin Ramadan, biyo bayan ayyana ranar Litinin 11 ga watan Maris, 2024, a matsayin ranar farko ga wata da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar III ya yi.

Jaridar SOLACEBASE  ta rawaito cewa ganin jinjirin watan daga sassa daban-daban na Najeriya shi ne farkon azumin watan Ramadan.

Karin labari: Gwamnatin Najeriya ta ce likitoci 16,000 ne suka tsere don aiki a Ketare

A wata sanarwa da mai baiwa mataimakin shugaban majalisar dattawa shawara kan harkokin yada labarai Ismail Mudashir ya fitar ta ce Barau ya bukaci al’ummar musulmi da su yi amfani da wannan wata mai albarka na Ramadan ta hanyar karfafa ibada da addu’o’i ga Allah Madaukakin Sarki.

Ya kuma bukaci masu hannu da shuni da kungiyoyi su rika tallafawa mabukata a cikin watan Ramadan da kuma bayansa kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya yi umarni.

”Ina maraba da shigowar wannan wata na Ramadan mai albarka bayan ganin jinjirin watan. Ramadan wata ne mai albarka na bautar Allah da neman gafara da taimakon mabukata.

Karin labari: Ma’aikatan jami’o’i sun ƙuduri shiga yajin aiki a Najeriya

“Kamar yadda muka sani, wannan lokaci ne da ya zo da dumbin lada, don haka akwai bukatar mu sanya kasarmu ta Najeriya da shugabanni a cikin addu’o’inmu na ci gaba da zaman lafiya da ci gaban al’ummarmu. Ba mu da wuri kamar Najeriya. Ramadan Kareem,” in ji shi.

A halin yanzu, mataimakin shugaban majalisar dattawan ya kammala shirye-shiryen raba shinkafa ga gidaje sama da 200,000.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here