Sama da sa’o’i ashirin bayan rushewar wani bene mai hawa daya da ke cikin sabuwar kasuwa ta Minna , an ci gaba da tantancewa da gyara gurin, amma babu wanda ya mutu a lamarin.
Wata sanarwa a ranar Asabar mai dauke da sa hannun Darakta Janar na Hukumar Ba da Agajin Gaggawa ta Jihar Neja, Abdullahi Baba’arah, ta ce na’urorin gano rayuwa na hukumar sun tabbatar da cewa har yanzu babu wanda ya makale a ginin da ya ruguje.
Babban Manaja na Hukumar Raya Birane ta Jihar Neja Bako Ismail ya kuma ce hukumar ta baiwa mai gidan wa’adin awanni 24 su kwashe kadarorin kafin su fara rusa ginin.