Sojoji Sun Kubutar Da Fararen Hula 386 Daga Dajin Sambisa Shekaru 10 Bayan Sace su

Some of the civilians rescued from sambisa forest by the army

Sojoji Sun Kubutar Da Fararen Hula 386 Daga Dajin Sambisa Shekaru 10 Bayan Sace su

Akalla mutane 386 ne akasari mata da kananan yara da Sojoji suka ceto a dajin Sambisa shekaru goma bayan sace su.

Mai rikon mukamin GOC 7 Division, Brig. Janar AGL Haruna, ya bayyana haka ne a lokacin da yake zantawa da manema labarai a wajen dajin Sambisa da ke karamar hukumar Konduga bayan ya karbi bakuncin sojojin da suka gudanar da aikin na kwanaki 10.

Haruna ya bayyana cewa, farmakin da aka yi wa lakabi da “Operation Desert Sanity 111” shi ne share dajin Sambisa da suka rage daga dukkan nau’ukan ‘yan ta’adda tare da samar da wasu daga cikin su masu kwadayin mika wuya kamar yadda aka samu damar yin hakan.

“Kokarin da muke yi shi ne mu tabbatar da cewa mun kawar da ragowar ‘yan ta’adda a Sambisa tare da baiwa masu son mika wuya su mika wuya.

“Da wannan aiki, muna sa ran da yawa daga cikinsu za su mika wuya kamar yadda suka fara.

“Mun kuma ceto wasu fararen hula; Ya zuwa jiya mun ceto 386 kuma na tabbata adadin zai karu zuwa yau,” inji Haruna.

GOC wanda ya yi wa sojojin jawabi kan sakon babban hafsan sojin kasar, ya yaba da kwazon da suka nuna a lokacin aikin, ya kuma bukace su da su ci gaba da gudanar da aikin.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here