Tinubu ya nemi majalisar dattawa ta tabbatar da Bosun Tijani a matsayin shugaban hukumar USPF

tinubu 2 (2)

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya roƙi majalisar dattawa da ta amince da nadin Ministan Sadarwa, Kirkire-kirkire da Tattalin Arzikin Fasahar Sadarwa, Bosun Tijani, a matsayin shugaban hukumar samar da ingancin sabis sadarwa ga kowa (USPF).

Tinubu ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa da shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya karanta yayin zaman majalisar a ranar Laraba, inda ya ce an gabatar da sunayen ne bisa tanadin sashe na 116 na dokar hukumar sadarwa ta ƙasa ta shekarar 2003.

A cikin wasiƙar, Tinubu ya nemi majalisar ta tabbatar da Tijani da wasu mutane takwas a matsayin shugabanni da mambobin hukumar, wadanda suka haɗa da Idris Olorunimbe a matsayin mataimakin shugaban hukumar, Abraham Oshidami, Rimini Makama, Aliyu Edogi Aliyu, Joseph B. Faluyi, Auwal Mohammed, Uzoma Dozie, Peter Bankole, Abayomi Anthony Okanlawon da Gafar Oluwasegun Quadri.

Shugaban ƙasa ya bukaci majalisar da ta yi la’akari da wannan buƙata cikin gaggawa domin gudanar da aikin hukumar ba tare da jinkiri ba.

Bayan karanta wasiƙar, shugaban majalisar dattawa Godswill Akpabio ya tura sunayen zuwa kwamitin sadarwa na majalisar, tare da umartar kwamitin da ya gabatar da rahoton bincikensa cikin mako guda.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here