Da ɗumi-ɗumi: Tinubu ya rantsar da Chris Musa a matsayin ministan tsaron Najeriya

e4ae37d3 2f0e 4aca 9a06 b33a403d8504.jpg

Shugaban ƙasa Bola Tinubu ya rantsar da Janar Christopher Musa a matsayin ministan tsaron bayan amincewar majalisar dattawa.

An yi bikin rantsar da tsohon babban hafsan tsaron ne a fadar shugaban ƙasa da ke Abuja ranar Alhamis, kwana ɗaya bayan ‘yan majalisar dattawan sun shafe kusan awa biyar suna yi masa tambayoyi yayin tantance shi.

Mai magana da yawun fadar shugaban ƙasa Bayo Onanuga ya wallafa hoton bikin rantsuwar a shafinsa na dandalin X.

BBC

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here