TUC ta ki amincewa da karin kashi 65% na kudin wutar lantarki

TUC

Kungiyar Kwadago ta kass (TUC) ta yi watsi da shirin karin kashi 65 cikin 100 na kudin wutar lantarki.

Matsayin TUC yana kunshe ne a cikin sanarwar da aka fitar a karshen taron kwata na farko na majalisar gudanarwa ta kasa (NAC) da aka gudanar ranar Alhamis a Abuja.

Da yake jawabi ga manema labarai bayan taron Festus Osifo, shugaban TUC, ya ce NAC a madadin majalisar ta yi Allah-wadai da karin kashi 65 na kudin wutar lantarki.

“Abin takaici ne yadda gwamnati ta yi la’akari da wannan yunkurin karin, yayin da karin da aka yi a baya ya jawo wa ‘yan kasa wahala sosai.

Karin labari: Kungiyar NLC ta dakatar da yunkurin ta zanga-zangabkan karin kudin kira da na Data

“Wannan karin da ake shirin yi ba kawai sakaci ba ne, har ma da gangan ne na zaluntar ’yan Najeriya kan tattalin arziki, wadanda tuni ke fafutuka cikin yanayin matsin tattalin arzikin da ba za a iya jurewa ba.

Osifo ya kara da cewa hukumar ta NAC ta kuma yi nazari a kan karin kashi 50 cikin 100 na kudaden harajin sadarwa da aka tsara, ta kuma amince da matsayar kungiyar kwadago ta Najeriya NLC, wajen yin watsi da matakin.

Shugaban na TUC ya ce an yanke shawarar kara harajin ne ba tare da la’akari da tasirin matsin tattalin arzikin da talakawa ke ciki ba.NAN

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here