Firaministan Indiya Modi ya gana da Tinubu a fadar Aso Rock 

Indian PM At Aso Villa 6 1

 

Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya ziyarci Fadar Shugaban Kasa ta Aso Rock a ranar Lahadi a yayin ziyarar aikinsa zuwa Najeriya.

Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu tare da wasu manyan jami’an gwamnati sun tarbi Modi da tawagarsa a cibiyar mulkin kasar.

Ana sa ran shugabannin biyu za su tattauna kan kara karfafa dangantaka tsakanin Najeriya da Indiya.

Wannan ita ce ziyarar farko da Firaministan Indiya ya kai Najeriya tun bayan ziyarar Dr. Manmohan Singh a shekarar 2007, lokacin da kasashen biyu suka kafa dangantakar hadin gwiwa ta musamman.

Zuwa Modi a ranar Asabar na nuna sabuwar manufa ta inganta alakar kasashen biyu.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here