Cibiyar kare hakkin yan jarida ta kasa da kasa ta yi Allah wadai da cin zarafin yan jarida da yan sanda suke a Kano

BREAKING 750x430
BREAKING 750x430

Cibiyar kare hakkin ‘yan jarida ta kasa da kasa IPC ta koka kan harin da aka kai wa ‘yan jaridan da ke sauraron karar zaben gwamnan jihar Kano.

Idan dai za a iya tunawa wasu ‘yan jarida biyu Salim Umar Ibrahim na Aminiya da kuma wakilin BBC Hausa, Zahraddeen Lawal, yan sandan dake aiki a kotun sun ci zarafin su, inda suka lalata kayayyakin aikinsu.

Melody Akinjiyan, jami’in hulɗa da jama’a na cibiyar ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba.

Sanarwar ta ce babban daraktan cibiyar ta IPC, Mista Lanre Arogundade, ya yi Allah wadai da cin zarafin yan jaridun da yan sanda sukai, ya kuma kara da cewa hana yan jaridu daukar rahoto tare da cin zarafin su ba dai dai bane, kuma yin hakan barazana ne ga dimokuradiyya.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here