Bauchi: Kotu Ta Tabbatar Da Nasarar Gwamna Bala Mohammed

Bala Bauchi sabo.jpeg
Bala Bauchi sabo.jpeg

Kotun sauraron kararrakin zaben gwamnan jihar Bauchi ta tabbatar da nasarar gwamna Bala Mohammed na jam’iyyar PDP a zaben gwamnan jihar da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar APC da dan takararta na gwamna, tsohon babban hafsan sojin sama, Air Marshal Sadique Abubakar suka shigar.

Ta ce babu wani kwakkwaran dalili na soke zaben saboda an gudanar da zaben ne bisa bin doka da oda.

Kwamitin mutum uku ne ya yanke hukuncin a karkashin mai shari’a P.T Kwahar.

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here