Atiku Ya Jagoranci Zanga-Zanga a Ofishin INEC 

PDP protest8 750x430 1
PDP protest8 750x430 1

Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP ya jagoranci zanga-zangar nuna kin amincewa da sakamakon zaben shugaban nasa na 2023. Atiku Abubakar na tare da sauran jiga-jigan PDP, ciki har da shugaban jam’iyyar na kasa, Ayu Iyorchia da gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal a helkwatan INEC da Abuja.

Sauran wadanda ke cikin zanga-zangar sun hada da; shugaban kwamitin kamfen na PDP, kuma gwamnan Akwa Ibom, Udom Emmanuel da dai sauran manyan masu fada a ji a jam’iyyar.

A tun farko, dan takarar na PDP ya ce bai amince da sakamakon zaben shugaban kasan da ya kawo Bola Ahmad Tinubu a matsayin wanda ya lashe zabe ba.

PDP da dan takarar sun zargi almundahana da siyan kuri’u a lokacin zaben na shugaban kasa.

 

AYI TSOKACI

Please enter your comment!
Please enter your name here